Kasar Ghana ta bayyana niyyar gina matatar man fetur ta biyu a kusa da matatar man fetur ta Tema (TOR) da ke aiki yanzu, in ji shugaba John Dramani Mahama a ranar Litinin a birnin Accra.
A cewarsa, gangar man fetur dubu 100 da ake sa ran samu a kowa ce rana (bpsd) na zuwa daidai da hangen Ghana na kasancewa wani ginshikin fitar da man fetur a yammacin Afrika.
TOR, babbar matatar man fetur ta Ghana, dake mallakar gwamnatin kasar na fitar da gangar man fetur dubu 60 a kowa ce rana, abin da ke biyan kawai kashi 50 cikin 100 na bukatun yau da kullum na cikin gida.
Haka kuma, bashi ya dabaibaye matatar tun yau da shekaru 10. A karshen shekarar 2015, wannan bashi ya kai kudin Cedis na Ghana biliyan 1,9, kimanin dalar Amurka miliyan 498,03.
Za mu zamanintar da tankokin mu na ajiyar mai, da kuma kara yawan man fetur da za mu iya samarwa da ajiyewa. Za mu aikatar da wannan matatar bakin gwargwado domin samar da ganga dubu 60 a kowa ce rana, kana daga baya mu kaddamar da aikinta gadan gadan, ta yadda za a samar da ganga dubu 100 a kowace rana, in ji shugaban kasar a gaban ma'aikatan TOR a yayin wata ziyarar aiki a wurin.
Mista Mahama ya yi wa ma'aikata alkawari cewa, gwamnati ba za ta rufe ido ba, kuma za ta tabbatar da ganin kome na gudana yadda ya kamata domin karfafa wannan sauyi. (Maman Ada)