in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Burundi ta yi Allah wadai da kisan da aka yiwa ministan kasar
2017-01-03 10:11:17 cri

Gwamnatin Burundi ta yi Allah-wadai da kisan da wasu 'yan bindiga suka yiwa ministan ruwa da muhalli na kasar Emmanuel Niyonkuru a ranar Lahadi da safe.

Kakakin gwamnatin Burundi Philippe Nzobonariba ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, gwamnatin Burundi tana juyayi da kisan da aka yiwa ministan nata. Kisan da a cewarsa yana daga jerin kashe-kashen da wasu bata gari ke yiwa jami'an gwamnati. Yanzu haka gwamnatin Burundin ta bukaci a gudanar da bincike don zakulo wadanda suka aikata wannan danyen aiki, tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Dan shekaru 54, an haife Emmanuel Niyonkuru ne a garin Rutegama da ke lardin Muramvya. Masanin tattalin arzikin, kana ministan ruwa, muhalli da tsara yankuna na kasar ta Burundi tun daga shekarar 2015 har zuwa lokacin da wasu 'yan bindiga suka halaka shi.

Tun a shekarar 2015 ne dai kasar Burundi ta tsunduma cikin rikicin siyasa, bayan da shugaba Pierre Nkurunziza ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takara a wa'adi na uku. Tun lokacin ne kuma ake ta kara samun tashe-tashen hankula a kasar, inda ake kaiwa manyan jami'an gwamnati hari.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China