in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana ya bukaci 'yan jaridun Afirka su daga matsayin nahiyar
2017-11-14 09:38:52 cri

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, ya bukaci 'yan jaridun nahiyar Afirka, da su rika yada bayanai game da abubuwan da ka iya daga martabar nahiyar a idon duniya.

Shugaba Akufo-Addo ya ce, 'yan jaridu na fuskantar kalubale da dama, kuma hakan ya sanya galibin labaran da ake fitarwa game da nahiyar, musamman ta kafofin kasashen waje ba masu dadi ba ne. Ya ce, sau da yawa a kan danganta nahiyar Afirka da tashe tashen hankula, da cututtuka, da talauci da kuma fari.

Shugaban na Ghana na wannan tsokaci ne cikin jawabin sa ga mahalarta taron yini 3, na masu ruwa da tsaki game da harkokin watsa labarai da ya gudana a birnin Accra.

Akufo-Addo ya kara da cewa, muddin dai talauci da rashin daidaito sun ci gaba da wanzuwa a nahiyar Afirka, abubuwan da za a ci gaba da yadawa game da nahiyar ke nan.

"Don haka, ku marubutan mu, 'yan jaridun nahiyar mu, kuna da nauyi mai yawa na kare martabar mu. Idan za ku yi rubutu, ya dace ya zama game da tarin damammakin da nahiyar ne ke da su, ba akasin hakan ba", a kalaman shugaban kasar ta Ghana.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China