in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yabawa tsarin ba da ilimin sakandare kyauta na Ghana
2017-09-14 10:10:39 cri

Mataimakin shugaban hukumar kula da ayyukan tarayyar Afrika AU Thomas Kwesi Quartey, ya yabawa kasar Ghana bisa aiwatar da tsarinta na ba da ilimi kyauta.

Da yake jawabi a wajen taron MDD kan cinikayya da ci gaba a Geneva na kasar Switzerland, Thomas Quartey ya ce, tsarin tarbiyar hanya ce ta tabbatar da ci gaban kasar, da ma Afrika baki daya.

Ya ce, kaddamar da tsarin a kasar zai kara karfafa manufar AU ta tabbatar da dukkan yaran Afrika na zuwa makaranta.

Thomas Quartey, ya ce burin AU ya zuwa shekarar 2020 shi ne, ganin kowanne yaro a Afrika na zuwa makaranta, inda ya ce, har ila yau, tana son samun nahiyar Afrika mai dauke da masu ilimi.

Gwamnatin kasar Ghana na da niyyar kashe miliyan 400 na cedi kwatankwacin dala miliyan 90.31 a kowacce shekara a kan tsarin.

Da yake kaddamar da shirin a birnin Accra, shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya ce, tsarin zai tabbatar da babu wani yaro da aka hanawa damar samun ilimin sakandare. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China