Yau Laraba Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, Sin na son hada kai da sabon sakataren harkokin wajen Amurka wajen ci gaba da raya huldar da ke tsakanin kasashen 2 ba tare da wata tangarda ba.
A jiya ne, shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da maye gurbin sakataren harkokin wajen kasar Rex Tillerson da Mike Pompeo, shugaban hukumar leken asiri na kasar wato CIA. (Tasallah Yuan)