Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya gana da shugaban Palestinawa Mahmoud Abbas ta wayar tarho, inda ya taya shi murnar daddale yarjejeniyar sulhu da kungiyoyin Fatah da Hamas suka yi.
Wata sanarwa da ofishin kakakin babban sakataren ya fitar, ta ce Antonio Gutarres ya yi farin ciki matuka bisa ci gaban da gwamnatin Palestinu ta samu a zirin Gaza, ya na mai jinjinawa gwamnatin kasar Masar bisa kokarin shiga tsakanin da ta yi kan batun.
Antonio Guterres ya ce, a shirye MDD take ta taimakawa gwamnatin Palestinu yayin da take gudanar da harkokin zirin Gaza, inda ya jaddada muhimmancin warware rikicin jin kai a zirin, musamman ma wajen samar da wutar lantarki, da jigilar kayayyakin jin kai.
Kungiyoyin Fatah da Hamas sun tattauna a birnin Alkahira na kasar Masar tsawon yini biyu, inda a jiya suka cimma yarjejeniyar sulhu.
Kungiyar Fatah ce za ta fara gudanar da harkokin zirin Gaza a maimakon Hamas tun daga ranar 1 ga watan Disamban dake tafe.(Jamila)