in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping: dole ne a aiwatar da manyan tsare-tsaren bunkasa yankunan karkara
2018-03-09 10:45:49 cri

Babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin soja na kasar Mr. Xi Jinping, ya ce aiwatar da manyan tsare-tsaren raya yankunan karkara, muhimmin aiki ne da JKS ta kaddamar a yayin babban taron wakilanta karo na 19, sannan babban aiki ne da ke kokarin raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi daga dukkan fannoni da kafa kasa ta zamani mai tsarin gurguzu daga dukkan fannoni.

Shugaba Xi Jinping wanda ya bayyana haka yayin da ya halarci taron tattauna rahoton aikin gwamnati da aka gabatar, wanda kungiyar wakilan jama'ar lardin Shandong ta shirya a jiya, ya kara da cewa, raya yankunan karkara gaggarumin aiki ne da zai bunkasa aikin gona da manoma yadda ya kamata, a wannan sabon zamani. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China