Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta sanar da cewa, kimanin mutane miliyan 3.1 a yankin arewa maso gabashin Najeriya ba su samu damar ziyartar asibitoci sakamakon rikicin Boko Haram da ya addabi shiyyar.
Cikin wani rahoton da ta fitar a birnin Maiduguri dake shiyyar arewa maso gabashin kasar, hukumar ta WHO ta ce, an lalata asibitoci da yawansu ya kai 755 a hare haren da mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram suka kaddamar a jihohi ukun da hare haren 'yan ta'addan suka fi kamari a shiyyar, da suka hada da jihohin Adamawa, Borno, da Yobe.
MDD ta sanar a watan Yulin shekarar 2017 cewa, kimanin adadin mutane miliyan 6.9 ne ke bukatar tallafin jin kai a shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar.(Ahmad Fagam)