in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta kara yawan haraji na barasa da taba
2018-03-12 09:34:50 cri

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar a jiya Lahadi cewa, za ta kara kudaden haraji na barasa da taba.

Ministar kudin kasar Kemi Adeosun ta ce, shugaban kasar Muhammadu Buhari shi ne ya amince da canza sabon farashin kudin harajin, kuma zai fara aiki ne daga ranar 4 ga watan Yunin bana.

A wata sanarwa da ta fitar, Adeosun ta ce, shugaban kasar ya kuma baiwa kamfanonin dake samar da kayayyakin wa'adin kwanaki 90 gabanin sabuwar dokar karin kudin harajin ta fara aiki.

Ta ce, domin daidaita tasirin farashin kayayyakin, sabon tsarin biyan harajin zai yi aiki ne na tsawon shekaru 3, wato tun daga shekarar 2018 zuwa 2020, saboda gwamnatin kasar tana neman kara kudaden harajinta na shekara.

A cewar ministar, sabon harajin da aka sanyawa tabar zai kunshi wanda ake karba a halin yanzu da kuma na musamman, kuma wanda ake kara a halin yanzun zai maye gurbin na musamman da ake karba daga bangaren barasa.

Ta ce, wannan mataki zai magance yadda ake samun bacewar kudaden harajin da gwamnatin ke karba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China