in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta kai tallafin kayayyakin jiyya a sansanin 'yan gudun hijira a Najeriya
2016-10-10 09:34:14 cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta kai tallafin gaggawa na kayayyakin kiwon lafiya a sansanonin 'yan gudun hijira 2 dake jihar Borno a Najeriya.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta WHO ta aikewa kamfanin dullancin labaru na Xinhua a Legas, ta ce, ta kai daukin ne sakamakon matsananciyar bukatar kayayyakin jiyya da ake da shi a sansanonin 'yan gudun hijira na Mafa da Dikwa, kuma biyu daga cikin yankuna 15 da dakarun Najeriya suka kwato daga hannun mayakan Boko Haram wadanda suke dauke da yawan al'umma kimanin 75,000.

Kayayyakin kiwon lafiyar sun hada da magunguna wadanda za'a yi amfani da su wajen jinyar mutane 15,000 cikin watanni uku.

Sakatare a ma'aikatar lafiya ta jihar Borno Abubakar Hassan ya yabawa tallafin da hukumar lafiyar ta bayar, ya kara da cewa, tallafin na WHO ya zo a daidai lokacin da ake bukatar sa.

Rex Mpazanje, jami'in hukumar WHO ya ce, hukumar a shirye take ta tallafawa jihar Borno da sauran jihohin shiyyar arewa maso gabashin kasar domin ci gaba da samar musu kayayyakin kiwon lafiya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China