in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta musanta batun gina masana'antar magunguna a Najeriya
2016-10-18 09:01:49 cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta musanta wani labari da jari'ar The Nation ta Najeriya ta wallafa, wanda ke cewa hukumar na shirin gina wani kamfanin harhada magunguna a jihar Imo dake kudu maso gabashin Najeriya.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta bayyana cewa, WHO ba ta shiga duk wata harka, wadda ta shafi kafa masana'antun hada magunguna, ko wata hada-hada ta cinikayya domin samar da riba. Kaza lika sanarwar ta jaddada manyan kudurorin hukumar da suka hada da tsara manufofi, da tabbatar da ana bin tsare tsare mafiya dacewa, wajen samar da muhimman magunguna da al'ummar duniya ke bukata.

Don gane da hakan ne hukumar ta WHO ta yi kira ga waccan jaridar da ta janye labarin da ta fitar, domin dakile barazanar da ka iya biyo bayan labarin ga jami'an hukumar dake Najeriya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China