in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta taimakawa Afrika samun ci gaba don tsayawa da kafafunta
2018-03-12 09:55:40 cri

Mataimakin ministan cinikin kasar Sin Qian Keming ya bayyana cewa, kasarsa za ta taimakawa kasashen Afrika wajen samun ci gaba, ta yadda za su iya tsayawa da kafafunsu a matsayin wani sabon mataki na kara kyautata dangantakar ciniki da tattalin arziki tsakanin Sin da kasashen na Afrika.

Qian ya fada wa taron manema labaran da aka shirya wa taro na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC ta 13 cewa, wannan mataki zai taimaka wajen rage talauci, samar da ayyukan yi, da kuma bunkasa tattalin arziki da kyautata rayuwar al'ummar Afrika, kana zai samar da horo da ayyukan yi, musamman ga matasan kasashen na Afrika.

Qian ya ce, baya ga muhimman ayyuka 10 na hadin gwiwar bangarorin biyu, wanda ya kunshi bunkasa masana'antu zuwa kiwon lafiya, wadanda aka ayyana su a taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wato (FOCAC) wanda aka gudanar a Johannesburg a shekarar 2015, kasar Sin tana tsara wasu sabbin matakai wadanda za su kara kyautata hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki bisa muradun da kasashen na Afrika ke da su.

Kasar Sin za ta gwama shawarar ziri daya da hanya daya, da ajandar ci gaba ta kungiyar tarayyar Afrika nan da shekarar 2063, da kuma sauran shirye shiryen ci gaba na daidaikun kasashen Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China