Wani kusa a gwamnatin kasar Sin ya ba da tabbacin kasar na kara yawan zuba jarin a kasashen nahiyar Afrika.
Mataimakin ministan harkokin kasuwanci na kasar Sin Qian Keming, ya tabbatar da hakan, ya ce, kasar Sin za ta fadada hannayen jarinta a Afrika, sannan za ta bunkasa hadin kai dake tsakaninta da kasashen na Afrika a sabbin fannonin tattalin arziki da suka hada da fannonin sufurin jiragen sama, da harkokin kudi, da yawon bude ido, da sufuri ta ruwa da kuma aikin gona.
Qian ya ce, ya yi amanna cewar, hadin kan dake tsakanin Sin da Afrika, zai kara habaka ci gaban bangarorin biyu, kamar yadda ya bayyana hakan a shirin tambaya da amsa na jaridar Economic Daily ta kasar.
A cewar wata kididdiga daga hukumomin kasar, a halin da ake ciki, kasar Sin ta zuba hannayen jari na sama da dalar Amurka biliyan 30 a Afrika daga shekarar 2014, adadin wanda ya ninka sau 64 idan aka kwatanta da shekara ta 2000, haka zalika yawan kudaden musayar cinikayya tsakanin kasar Sin da Afrika ya tasamma dala biliyan 222, wanda ya ninka sau 20 daga shekarar ta 2000.(Ahmad Fagam)