Wakilin kasar Sin a MDD, ya bukaci a kara zuba jari a kasashen dake yankin babban tafkin nahiyar Afrika, ta hanyar yin hadin gwiwa don samun ci gaba.
Mista Liu Jieyi, wakilin din din din na kasar Sin a MDD, ya ce, wannan yanki yana tsakiyar Afrika, amma sakamakon matsalar tabarbarewar tsaro ya haifar da koma baya a yankin, sannan al'ummomi mazauna yankin suna fama da wahalhalun rayuwa.
A yayin da yake jawabi a taron kwamitin sulhun MDD, Liu, ya jaddada bukatar dukkan bangarori da su gudanar da aiki tare domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya, ta hanyar hadin gwiwa a jamhuriyar demokaradiyyar Congo wanda aka cimma yarjejeniya kan ta da yankin a watan Fabrairun shekarar 2013.
A ta bakin mista Liu, kasar Sin tana maraba da duk wani yunkurin hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya da samar da tsaro, sai dai ya danganta matsalar yawan tashe tashen hankulan a wasu sassan na yankin babban tafkin da cewar, talauci da koma baya ne suka haddasa.
Wakilin na Sin ya ce, a ko da yaushe, kasar Sin a shirye take ta hada gwiwa da kasashen Afrika a fannoni da suka hada da ci gaban masana'antu, da noma, da fannin kudade, da yaki da fatara, da kiwon lafiya, da samar da kayayyakin more rayuwa, da raya al'adu da kuma samar da zaman lafiya da tsaro.
Liu ya kara da cewa, kasar Sin ta shirya tsab, domin hada gwiwa da Afrika game da kudurorin da aka cimma a taron dandalin hadin kan Sin da Afrika da aka gudanar a watan Disambar shekarar 2015 a Johannesburg, wanda zai ciyar da rayuwar al'ummar Afrika gaba.(Ahmad Fagam)