Jiang Zengwei, shugaban hukumar kasar Sin mai kula bunkasa cinikayya na kasa da kasa, ya ce, kasar ta ci gaba da kasancewa babbar aminiya ga nahiyar Afrika ta fuskar cinikayya da bunkasa ci gaban tattalin arziki.
A lokacin wani taron tattaunawa game da zuba jari tsakanin Sin da kasar Sao Tome da Principe a Juma'ar da ta gaba a birnin Beijing, Jiang ya ce, ya zuwa shekarar 2016, huldar cinikayya dake tsakanin Sin da Afrika ya tasamma dalar Amurla biliyan 149.1.
Jiang ya ce, dangantakar kasuwanci tsakanin Sin da Afrika tana ci gaba da samun bunkasuwa, sannan akwai kyakkyawar fahimtar juna ta fuskar zuba jari, kana kamfanonin kasar Sin sun zuba jarin da ya tasamma dala biyan 3 da miliyan 200 a nahiyar ya zuwa shekarar 2016.
Ya ce, galibin kamfanonin na Sin sun zuba jarinsu ne a fannonin da suka hada da gine gine, ayyukan hidima, ma'adanai, aikin gona da samar da kayayyakin more rayuwa, kuma jarin zai amfanar tare da samar da ci gaban dukkan bangarorin biyu wato Afrika da Sin.
Game da Sao Tome da Principe, Jiang ya ce, a matsayin Sin na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kasar za ta ci gaba da samar da kudade domin bunkasa masana'antu da samar da kayayyakin fasahar zamani domin tallafawa ci gaban tattalin arziki da rayuwar al'ummar kasar ta Afrika(Ahmad Fagam)