in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uganda ta gabatar da sunayen 'yan wasan kasar da za su halarci gasar wasannin Commonwealth
2018-03-06 19:17:41 cri
Hukuma mai kula da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Uganda ta gabatar da sunayen 'yan wasa 23 wadanda za su halarci gasar wasannin Commonwealth da za ta gudana a Gold Coast na kasar Australia.

Yayin da yake magana da manema labaru, Dominic Otuchet, shugaban hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Uganda, ya ce yana da kwarin gwiwa game da ingancin kwarewar 'yan wasan da aka zaba, saboda haka yana sa ran ganin sun dawo da lambobin yabo.

Moses Kipsiro, dan wasan da ya taba samun lambobin yabo guda 3 a gasar ta Commonwealth, shi ma yana cikin 'yan wasan da aka zaba, inda zai shiga gasar tseren mita dubu 10, domin kare lambar zinariya da ya lashe yayin gasar da ta gudana a baya a Scotland na kasar Birtaniya.

Gasar ta Commonwealth tana hallara dukkan kasashe ko yankuna mambobin kungiyar Commonwealth wato kasashe renon Ingila. Gasar da ake sa ran gudanarwa daga ranar 4 zuwa 15 ga watan Afrilu mai zuwa a Gold Coast din kasar Australia.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China