in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Serena Williams tana shirin komawa wasa
2018-03-06 19:11:55 cri
Shahararriyar 'yar wasan tennis ta duniya Serena Williams, mai shekaru 36 a duniya, tana shirin fatawa a gasar 'yan wasa daya daya ta BNP Paribas Open, wadda za ta gudana a filin wasan tennis na Indian Wells dake kasar Amurka cikin wannan mako.

'Yar wasan wadda ta haifi diyarta na farko watanni 6 da suka wuce,ba ta halarci wata babbar gasa ba tun bayan gasar Australian Open da ta gudana a shekarar 2017, saboda cikin Alexis da ta ke dauke da shi. 'Yar wasan da ta lashe manyan lambobin yabo a wasan tennis har karo 23 na tare da burin zama mace ta farko wadda ta lashe kambi a gasar Indian Wells har karo 3, wato bayan nasarorin da ta samu a shekarar 1999 da 2001.

Rahotanni na cewa, Serena Williams da yayarta Venus Williams ka iya karawa da juna a zagaye na 3 na gasar ta wannan karo. Kana Serena za ta fafata da Zarina Diyas 'yar kasar Kazakhstan a zagayen farko na gasar. Diyas mai shekaru 24 a duniya, tana matsayi na 53 a duniya. Sai dai a gasannin 2 da suka fafata, Serena ta doke ta sau 2 a jere.

Serena ta yi fama da wasu 'yan matsaloli na rashin lafiya bayan da ta haifi diyarta, lamarin da ya hana ta damar halartar gasar Australian Open ta waccan shekara.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China