Wannan shine karo na biyu da dan wasan na Spaniya ya samu lambar yabon a babban birnin kasar Sin, tun bayan wadanda ya samu a shekarar 2005 a lokacin da ya doke Guillermo Coria dan kasar Argentina.
Nadal ya fada bayan kammala gasar cewa, "wannan shine irin matsayin dana samu a shekarar 2005. A shekarar ta 2005 ban taba tsammanin cewa zan cigaba da wasan kwallon tennis har zuwa shekarar 2017 ba," "murnar da nake ta bana, tafi kowacce. Abu na farko wasannin da aka gudanar sun fi wadanda aka yi a shekarar 2005 girma. Kusan wasanni 500 ne. A lokutan baya wasannin 250 ne ko kuma 175 ake gudanarwa.
Nadal ya cigaba da cewa, "Na gamu da wahala a wannan karon. A lokacin da naga mun yi kunnen doki a wasannin, na sani cewa abune mai matukar wahala na samu nasara a wannan karon. Amma nayi nasara a ranar farko, inda na samu maki har biyu. Daga bisani na yi tunanin cewa nayi wasa mai kyau a wannan shekarar, nayi wasa mai matukar kyau a wannan karon, na yi zarra akan abokan karawata masu wahalar sha'ani".(Ahmad Fagam)