Gwamnatin kasar Sin a yau Litinin ta gabatar da wani rahoto ga hukumar kolin kasar, inda ta yi nuni da cewa, a bana akwai manyan ayyuka guda 3 da dole ne kasar Sin za ta kammala su da kyau, wato yin rigakafi da shawo kan hadaruka masu tsanani yadda ya kamata, kara karfin yaki da talauci ta hanyar kimiyya da sa kaimi kan kara samun ci gaba wajen yaki da gurbata muhalli. (Tasallah Yuan)