Za'a yi zaman taron farko na majalisar CPPCC karo na 13 daga ranar 3 zuwa 15 ga watan Maris
Da karfe uku na yammacin gobe Asabar, za'a kaddamar da zaman taro na farko na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin(CPPCC) karo na 13 a birnin Beijing, kana za a rufe taron da safiyar ranar 15 ga watan da muke ciki. Mai magana da yawun zaman taron Mista Wang Guoqing ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai na gida da na waje a yau Jumma'a.
Majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, CPPCC a takaice, hukumar musamman ce dake bayar da shawarwari game da harkokin siyasar kasar, da sa ido kan harkokin kasa bisa tafarkin demokuradiyya, tare kuma da shiga cikin harkokin siyasar.
Wang ya kara da cewa, an shirya tsaf don gudanar da zaman taron na wannan karo.(Murtala Zhang)