Kamar yadda kamfanin dillancin labaru na Reuters na kasar Birtaniya ya bada labarin cewa, shawarar da kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya gabatar ta nuna niyyar yin amfani da tsarin mulki wajen gudanar da mulki, inda aka mai da aiwatar da tsarin mulki abu mafi muhimmanci cikin yunkurin kasar na gudanar da harkokin mulki bisa doka.
A nasa bangare, kamfanin dillancin labaru na Tars na kasar Rasha ya ce, ana neman gyaran tsarin mulkin kasar Sin ne don baiwa kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin damar kara taka rawa a fannonin hadin kan mambobin jam'iyyar, da al'ummomin kasar daban daban, da neman samun walwala a kasar daga dukkan fannoni.(Bello Wang)