in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Batun yiwa kundin tsarin mulkin gyaran fuska na kan gaba a ajandar taron JKS dake tafe
2017-12-27 19:49:39 cri

A wani labarin kuma, wata sanarwa da aka fitar bayan kammala taron sashen siyasa na kwamitin kolin na JKS da Xi Jinping ya jagoranta a Larabar nan ta bayyana cewa, za a tabbatar cewa, ana ci gaba da tafiyar da harkokin jam'iyya bisa doka da kuma yaki da cin hanci.

Sanarwar ta kara da cewa, kwamitin ladaftarwa da sanya ido na kwamitin koli yana sanya ido kan mambobin jam'iyya yadda ya kamata, da daukar matakan ladaftarwa kan wadanda suka aikata ba daidai ba bisa tunanin Xi Jinping na tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki.

Muddin ana bukatar kwalli ta biya kudin sabulu a yakin da ake yi da cin hanci da rashawa, kwamitin ladaftarwa da sanya ido na CCDI zai yiwa tsarin sanya ido da yaki da cin hanci da rashawa a kananan matakai gyaran fuska, kamar yadda sanarwar ta bayyana. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China