in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Beijing ya fitar da sabbin matakan jan hankalin kwararru daga kasashen waje
2018-02-28 10:04:00 cri

Gwamnatin birnin Beijing ta fitar da sabbin matakan jan hankalin karin kwararru 'yan kasashen waje, musammam zuwa babbar cibiyarta ta kimiyya ta Zhongguancun Science Park.

Daga cikin sabbin matakan 20, 5 na da nufin saukaka shige da ficen baki kwarraru a birnin, ciki har da saukaka abubuwan da ake bukata na samun izinin zama na din din din.

Matakai 6 kuma na da nufin daukaka hanyoyin daukar aiki da amfani da kwararrun, yayin da sauran 4 kuma ke mayar da hankali wajen samar da ingantattun hanyoyin fara sana'a da kyakkyawan yanayi kirkire-kirkire ga baki ma'aikata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China