in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kafa karamin ofishin kula da harkokin mulki a Tongzhou da ke nan birnin Beijing
2015-07-13 10:40:49 cri

An bayyana a gun taron cikakken zama na kwamitin jam'iyyar kwaminis ta Sin na birnin Beijing karo na 17 wanda aka rufe a rana Asabar cewa, za a gaggauta kafa karamar cibiyar kula da harkokin mulki a unguwar Tongzhou, don tantance yawan mutanen da ke birnin Beijing, wanda ba zai wuce miliyan 23 ba kafin shekarar 2020, yawan mutanen dake kwaryar birnin Beijing zai ragu da kashi 15 cikin dari.

Taron ya bayyana cewa, birnin Beijing zai tantance yawan mutane ne ta hanyar sa-ido kan masana'antu da gidaje, domin samar da tsarin rayuwar da ta dace ga jama'a. Wasu kwararru sun bayyana cewa, an canja matsugunin karamar cibiyar kula da harkokin mulki ta birnin Beijing ce domin tabbatar da shirin bunkasuwar biranen Beijing da Tianjin da Lardin Hebei gaba daya, da kuma rage yawan cunkoson jama'ar da ake fuskanta a birnin.

Bugu da kari, kwararru sun kara da cewa, gwamnati da sassa daban daban na al'ummar birnin Beijing sun cimma matsaya daya kan kafa cibiyoyi a wurare daban daban domin magance matsalolin yawan jama'a da zirga-zirga da kuma karancin abubuwan more rayuwa.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China