in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Daliban Afrika ta Kudu za su karbi horo kan fasahar sadarwa a Sin
2017-10-13 12:36:24 cri

Jami'an kasar Sin da na Afrika ta Kudu sun yi wa wasu dalibai 10 da aka yi wa lakabi da 'manyan gobe' bankwana, inda suka shirya don tahowa kasar Sin da nufin samun horo kan fasahar sadarwa.

Nan ba da jimawa ba ne daliban za su fara karbar horon na tsawon makonni biyu.

Wadannan dalibai sun karanci darrusa daban-daban a fannin fasahar sadarwa a wasu jami'o'i dake fadin kasarsu, ciki har da jami'ar fasaha ta Tshwane da jami'ar North West da jami'ar fasaha ta Durban da jami'ar fasaha ta Tsakiya da kuma jami'ar Nelson Mandela.

Yayin tafiyar ta makonni biyu da za su karbi horo tare da fahimtar al'adun kasar Sin, za a horar da daliban kan fasahohin zamani na hanyoyin sadarwa da manhajoji da rumbun adana bayanai na kamfanin Huawei da ya dauki nauyin shirin. Baya ga haka, za su samu damar gano al'adun gargajiya na Sinawa da wuraren tarihi kamar Bangon duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China