in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cutar murar tsuntsaye na ci gaba da yaduwa a Afrika ta kudu
2017-09-11 11:03:45 cri

Hukumomi a Afrika ta Kudu sun ce, cutar murar tsuntsaye na ci gaba da yaduwa a kasar, inda aka samu barkewarta a larduna 6 daga cikin 9.

A cewar hukumar kula da harkokin gona da dazuka da kiwon kifi ta kasar DAFF, kawo yanzu, an kebe tsuntsaye sama da 600,000.

Barkewar cutar murar ta baya-bayan nan ta jefa fargaba a bangaren kiwon dabbobin gida na kasar tun bayan gano ta da aka yi a watan Yuni. Kafin wancan lokaci, ba a taba samun barkewar cutar ba.

Hukumar ta DAFF ta ce, gwamnati da bangaren masu sana'ar kiwo sun hada hannu wajen lalubo nagartattun matakan kimiyya da za a iya aiwatarwa domin dakile yaduwar cutar, tare da rage tasirinta ga dabbobi a Afrika ta Kudu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China