in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
COSATU ta bukaci gwamnatin da ta shirya taron warware matsalar karancin ayyukan yi
2017-06-29 09:22:02 cri

Gamayyar kungiyoyin 'yan kwadago a Afirka ta kudu ko COSATU a takaice, ta bukaci gwamnatin kasar da ta shirya wani taron masana, wanda zai mai da hankali ga zakulo hanyoyin magance matsalar karancin guraben ayyukan yi dake addabar al'umma.

Da yake tsokaci game da wannan batu, kakakin kungiyar na kasa Sizwe Pamla, ya ce yawaitar masu zaman kashe wando, wanda yanzu haka ya doshi kaso 27 bisa dari na daukacin 'yan kasar babban kalubale ne ga gwamnatin jam'iyyar ANC mai mulki, wanda kuma ya dace a gaggauta shawo kan sa.

Kiraye kirayen dai sun biyo bayan wasu alkaluman kididdiga da aka fitar a ranar Talata, wadanda ke nuna cewa, ya zuwa watanni 3 na baya bayan nan, mutane kusan 50,000 ne suka rasa guraben ayyukan su a kasar, adadin da kuma ya kai kusan mutane 60,000 a shekarar da ta gabata.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China