Bisa bayanan da majallar Fast Company ta gabatar, kamfanin mafi girma a fannin samar da motocin wutar lantarki ba kamfanin Tesla na kasar Amurka ba, a hakika shi ne kamfanin BYD na kasar Sin. Kamfanin, wanda ma'anar takensa ita ce "Cimma burinka", ya fara da samar da batir. Daga bisani ya yi amfani da fasahohin da ya samu a wannan fanni domin tsara tare da samar da motocin wutar lantarki, tun da yadda irin wannan mota za ta yi aiki na dogaro kan ingancin batir da aka ajiye a cikinta.
A nata bangaren, Stella Li, babban darektan kamfanin BYD mai kula da harkokinsa a yankin arewacin nahiyar Amurka, ta ce, tana alfahari da kyautar da kamfaninta ya samu a wannan karo. A cewar ta, kamfanin BYD yana tsayawa kan kokarinsa na kirkiro sabbin fasahohi a fannin makamashi, wadanda suke da inganci, da tsaro, gami da dorewar aiki.(Bello Wang)