180301-Sinawa-na-kara-shaawar-wasannin-kankara-zainab.m4a
|
Yanzu haka akwai filayen wasannin kankara a kewayen birnin Beijing, inda masu sha'awar wasannin kankara da dama ciki har da matasa da yara su kan je a lokacin hunturu. Wani dalibi dake zuwa filin wasan kankara na Shijinglong dake birnin Beijing tare da abokan karatunsa ya bayyana cewa, abokan karatunsa ne suka fara kai shi wajen wasan zamiyar kankara. Ko da yake bai kware a wasan ba, amma yana sha'awar wasan sosai, ya ce yanzu ya iya wasa, kana ya iya motsa jiki. Kasar Sin tana kokarin ganin mutane miliyan 300 sun iya wasannin zamiyar kankara, yana son zama daya daga cikinsu.
Manajan filin wasan a kan kankara na Jundushan Qiao Wei ya bayyanawa 'yan jarida cewa, Sabo da birnin Beijing ya samu iznin daukar bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na shekarar 2022, shi ya sa yana fatan mutane sun mayar da hankali ga sha'awar motsa jiki, ta yadda yawan masu sha'awar wasa a kan kankara zai karu sosai.
An shafe fiye da shekaru 10 ana wasan kankara a birnin Beijing, mutane da dama sun san wasan ba ya bukatar kashe kudi da dama, kana gwamnatin birnin ta kara fadakar da mutane game da wasan, don haka karin mutane suke son gwada wannan wasa, musamman matasa.
Shugabannin hukumomin da abin ya shafa na birnin Beijing sun bayyana cewa, dalilin da ya sa karin matasa da yara suke halartar wasanni a kan kankara shi ne yadda wasanni ke janyo hankalin iyayen yara, wadanda suka fi son wasanni. Sun ce, kamar yadda ake tura yara su koyi wasan kwallon kwando ko wasan piano, iyayen yara suna son yaransu su motsa jiki da samun abokai ta hanyar wasanni a kan kankara. Kana wasu iyayen yara su kan tura yaransu da su yi wasanni a kan kankara.
Zhao Qixiang, mai shekaru 7 da haihuwa, ya fara yin wasa a kan kankara tun a wannan shekara, ya ce, yana sha'awar wasannin kankara, iyayensa sun tura shi wani kwas na koyon wasan kankara. Iyayensa sun bayyana cewa, a halin yanzu, yawan kudin da a kan biya don koyon fasahohin wasa a kan kankara ya kan kai kimanin dala 27 a ko wace awa a birnin Beijing, ban da kudin hayar kayayyakin wasan. Mahaifiyar Qixiang ta bayyana cewa, danta ya koyi dabarun wasan yadda ya kamata bayan da ya shiga kwas din.
Ban da mazauna birnin Beijing, mutane daga sauran wuraren kasar Sin su kan zo filayen wasan kankara dake birnin Beijing. Wasu suna zuwa birnin Beijing yawon shakatawa da yin wasan kankara ne. Ana iya ganin mutane daga kudancin kasar Sin kamar lardin Guangdong, da Jiangsu da kuma birnin Shanghai da suka zo nan don yin wasanni a kan kankara. Bayanai na nuna cewa, wasu mutane su kan zo filayen wasan kankara kai tsaye ta layukan jiragen kasa.
Kamar yadda suka yi a shekarun baya baya nan, adadin mutanen da suke yin wasanni a kan kankara a birnin Beijing ya fi yawa a hutun ranar 1 ga watan Janairu da kuma hutun bikin bazara. Kana adadin ya karu sosai bisa na shekarar da ta gabata.
Tun bayan da kasar Sin ta samu nasarar karbar bakuncin gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2022, hankalin Sinawa ke kara karkata ga wasanni a kan kankara. Hukumar raya yawon shakatawa ta birnin Beijing ta bayyana cewa, yawan masu yawon shakatawa da suka ziyarci filayen wasan kankara na birnin Beijing a hutun bikin bazara na shekarar 2017 ya kai dubu 84, wanda ya karu da kashi 8.6 cikin dari bisa na shekarar 2016. Ta kuma yi imani da cewa, yawansu a hutun bikin bazara na shekarar 2018 zai ci gaba da karuwa.
A matsayin daya daga cikin ayyukan da aka yi alkawarin gudanar da su yayin da kasar Sin take neman iznin karbar bakuncin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu, kasar Sin ta yi alkawarin ganin mutane miliyan 300 sun halarci wasanni a kan kankara. Tun bayan da birnin Beijing na kasar Sin ya yi nasarar daukar bakuncin gasar ta shekarar 2022, ana iya ganin mutane da dama dake zuwa wasanni a kan kankara. Yawan masu yawon shakatawa da suka zabi yin wasanni a kan kankara a kasar Sin ya karu sosai, ciki har da yara da dama da suka koyi fasahohin wasa a kan kankara. A sakamakon damar daukar bakuncin gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu da kasar Sin ta samu, Sinawa za su kara shiga wasanni a kan kankara.
A halin yanzu, yawan filayen wasan kankara a kasar Sin ya zarce 500, sabanin 200 kawai a shekarar 2010.
Ban da karuwar yawan filayen wasan kankara, ana kuma bullo da ayyukan yau da kullum don shirya gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2022. Nan gaba kadan za'a fara aikin gina layin jirgin kasa mai saurin tafiya a Zhangjiakou dake arewacin kasar Sin, daya daga cikin biranen da za su karbi bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu a shekarar 2022 tare da hadin gwiwar birnin Beijing.
Tashar kudancin Zhangjiakou ta yi jigilar fasinjoji sama da miliyan 20, tun daga lokacin da ta fara aiki a shekarar 1957. Tashar ba za ta iya biyan bukatun yawan fasinjojin dake karuwa a kullum a yankin ba.
Ana saran za'a kammala aikin layin dogo mai saurin tafiya mai nisan kilomita 174 daga Beijing zuwa Zhangjiakou nan da shekarar 2019, inda za'a rage tsawon lokacin da ake shafewa wajen zirga zirga tsakanin biranen biyu daga sa'o'i uku zuwa mintoci 50.
Wadannan ayyuka sun shaida cewa, an samu nasarar daukar bakuncin gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu, kasar Sin tana kokarin gudanar da shirye-shirye yadda ya kamata, kana ana kokarin cika alkawarin ganin mutane miliyan 300 sun shiga wasanni a kan kankara, kuma yanzu haka Sinawa suna sha'awar wannan wasa.
Shugaban hukumar wasanni ta kasar Sin Gou Zhongwen ya bayyanawa 'yan jarida cewa, yanzu haka an fi mayar da hankali wajen ilimantar da matasa da yara shiga wasanni a kan kankara. Za a shigar da darussan koyar da wasanni a kan kankara a makarantu, wannan zai taimakawa matasa da yara fahimta da kara shiga irin wadannan wasanni.
A karon farko, kasar Sin za ta karbi bakunci shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2022. Kuma Sin tana shirye-shiryen gasar yadda ya kamata, kana hankalin jama'ar kasar Sin ya kara karkata ga wasanni a kan kankara, inda yanzu haka suke son shiga irin wasanni da kansu. An yi imani cewa, za a kara raya wasannin kankara a kasar Sin a sakamakon iznin da kasar ta samu na daukar bakuncin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu. (Zainab Zhang)