in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya yiwa al'ummar Sinawa fatan alheri domin murnar bikin bazara
2018-02-14 20:47:25 cri
A safiyar yau Laraba ne kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma majalisar gudanarwa ta kasar, suka shirya wani bikin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ta shekarar 2018, inda Mr. Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar, kuma shugaban kasar, sannan shugaban kwamitin koli na sojin kasar ya gabatar da wani muhimmin jawabi, inda yake cewa, "dole ne mu tsaya ga manufarmu tare da nauyin dake bisa wuyanmu, domin kokarin bude wani sabon shafin tarihi dake bayyana yadda al'ummomi Sinawa biliyan 1.3 suke kokarin neman ci gaba".

Sannan a madadin kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da majalisar gudanarwa ta kasar, shugaba Xi Jinping ya gabatar da fatan alheri a sabuwar shekara ga al'ummomin kabilu daban daban, da 'yan uwa na yankin musamman na Hongkong da Macao, da kuma na Taiwan, da kuma wadanda suke da zama a ketare.

A dakin taron jama'a na Beijing, mutane nagarta fiye da dubu 2 wadanda suka fito daga bangarori daban daban na kasar Sin sun taru domin shagalin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China