in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yang: Ya kamata addini ya dace da yanayin al'ummar Sinawa
2018-02-12 09:02:20 cri

Mataimakin firaministan kasar Sin kana mamba a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS Wang Yang ya jaddada cewa, wajibi ne yadda ake tafiyar da harkokin addinai a kasar Sin ya dace da tsarin gurguzu na al'ummar Sinawa.

Wang wanda ya bayyana hakan yayin taron karawa juna sani da shugabannin kungiyoyin addinai na kasar gabanin bikin bazara, bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, ya ce akwai bukatar shugabannin addinai dake kasar Sin su kara nazartar tasirin sakamakon babban taron wakilan JKS karo na 19 da aka kammala, kana su yi wa kungiyoyin addinai jagora, ta yadda za su dace da yanayin al'ummar Sinawa dake bin tsarin gurguzu.

Jami'in na kasar Sin ya kuma yaba da irin rawar da kungiyoyin addinai ke takawa wajen yayata akidar hadin kai tsakanin kabilun kasar da ci gaban harkokin addini da zaman jituwa tsakanin al'ummu.

Su ma wakilan kungiyar addinin Buddha na kasar Sin, da Taoi da na addinin Musulunci da kungiyar darikar Katolika da gammayar kungiyoyin majami'u na darikar Protestant sun gabatar da jawabai yayin wannan taro. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China