in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a shirya dandalin zaman lafiya ta hanyar tattaunawar addinai na ECOWAS a Niamey
2016-11-17 10:23:50 cri

Babban birnin Nijar, Niamey zai karbi bakuncin dandalin farko na gamayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) kan zaman lafiya, bisa hanyar tattaunawar addinai daga ranar 22 zuwa 23 ga watan Nuwamba, in ji ministan al'adun kasar Nijar Malam Issa Assoumana a ranar Laraba.

Dandalin na da burin tabbatar da ci gaban tattalin arziki da dunkulewar al'ummar kasashe mambobin ECOWAS goma sha biyar, yankin dake fama da rikice rikice da tashen tashen hankalin siyasa, al'umma, kabilanci da na addinai a halin yanzu, in ji ministan.

Haka kuma, dandalin na fatan tattara dukkan bangarori daban daban na addinai, ta yadda za'a kafa wata tattaunawa ta tsakanin addinai, ingiza dangantaka mai armashi tsakanin addinai, da tattauna zaman lafiya ta hanyar fadakar da mabiya addinai kan wajabcin gina wata al'adar zaman lafiya, da cusa wa shugabannin addinai wata al'adar tattaunawa dake tsakanin addinai domin samun ci gaban al'umma. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China