A kwanakin baya ne, kwamitin kula da 'yancin addini na kasar Amurka ya gabatar da rahoto na shekarar 2017, inda ya bada shawarar ci gaba da maida kasar Sin a matsayin kasar da aka fi maida hankali. Game da wannan batu, Geng Shuang ya bayyana cewa, jama'ar kasar Sin daga kabilu da sassa daban daban suna da cikakken 'yancin yin addinin da suka ga dama. Wannan kwamitin ya nuna bambanci ga kasar Sin kuma ta kyale ci gaban da Sin ta samu a fannin addini, kuma ya sha ba da rahotonni na shafa wa kasar Sin bakin fenti ta fannin 'yancin addini. Ya kamata ya girmama hakikanin halin da ake ciki kana ya yi watsi da ra'ayin kuskure, da daina tsoma baki a harkokin cikin gida na kasar Sin ta hanyar batun addini. (Zainab)