in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Al'amurra sun ta'azzara a Gaza sakamakon rashin damar shigar da tallafi
2017-11-20 11:25:21 cri
Mai magana da yawun hukumar bada agaji ta MDD dake taimakawa 'yan gudun hijirar Palastinu (UNRWA) Christopher Gunness, ya yi gargadin cewa al'amurra na cigaba da tabarbarewa a hukumar ta UNRWA da kuma zirin Gaza.

UNRWA, wanda ta kasance kungiyar bada jin kai mafi dadewa a duniya, ta kasance cikin mawuyacin hali sakamakon karancin kudaden gudanarwa da take fuskanta saboda karuwar adadin mutanen dake neman agaji a yankin ya zarta karfin da hukumar ke dashi na agazawa al'ummar Palastinawa dake neman dauki daga hukumar ta UNRWA.

A wata hira ta musamman da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Gunness ya bayyana cewa, har yanzu ba'a samo bakin zaren warware matsalar da Palastinawa 'yan gudun hijrar suke ciki tare da iyalansu ba.

Ya ce a halin da ake ciki suna fuskantar gibin kudade da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 77 a cikin kasafin kudin da suka tsara, wanda a cewarsa wannan abu ne da ba za'a taba laminta ba.

Gunness ya ce, a halin da ake ciki yankin zirin Gaza yana cikin wani yanayi na tsananin rashin samun damar shiga daga dukkan bangarorin wanda ya hada da bangaren kasar Masar da Isra'ila, kana yamma da kogin Jordan yana cigaba da fuskantar mamaya. A cewarsa akwai tsananin bukatar shigar da kayayyakin jin kai, wanda alummar Palastinawan suke cikin halin bukata, lamarin da ya sa hukumar UNRWA take neman karin kudaden gudanar da ayyukanta na bada agaji.

Mai magana da yawun hukuamr ta UNRWA da wasu jami'an MDD, sun sha nanata yin gargadi game da tabarbarewa al'amurra a zirin Gaza, wanda Gunness ya bayyana cewa hakan na faruwa ne a sanadiyyar rashin samun damar kai dauki yankin, inda yace a halin da ake ciki jama'a masu yawa suna kai musu korafe-korafen rashin samun tallafin abincin da zasu ci.

Gunness ya ce, shi da kansa ya mika bukatar neman agajin ga kasar Sin, sabo da irin rawar da take takawa a duniya, kasancewa ya taba yin aiki a matsayin dan jarida, inda ya bayyana cewa hadin gwiwar da kasar Sin da UNRWA suka yi wajen bada taimako ya taimaka matuka a halin yanzu. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China