in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da Theresa May
2018-02-01 20:42:35 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministar kasar Burtaniya Madam Theresa May yau Alhamis a nan birnin Beijing.

Xi Jinping ya isar da gaisuwarsa da fatan alheri zuwa ga sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ga Theresa May, ya kuma bayyana cewa, tun bayan da Sin da Burtaniya suka kulla huldar jakadanci tsakaninsu ya zuwa yanzu, hadin-gwiwar kasashen biyu ta samu dimbin nasarori.

Shugaban ya kara da cewa, a shekara ta 2015, ya yi nasarar kai ziyara Burtaniya, abun da ya bude wani sabon babi na ci gaban alakokin kasashen biyu. Kana kasar Sin na son yin kokari tare da Burtaniya don kara raya huldodinsu a cikin sabon yanayi, da kara samar da alfanu ga jama'arsu, gami da tabbatar da samun bunkasuwa da zaman lafiya a duk fadin duniya baki daya.

A nata bangaren, Madam Theresa May ta isar da gaisuwar sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu zuwa ga shugaba Xi, tana mai cewa, Burtaniya da Sin na da ra'ayoyi masu yawa dake kama da juna dangane da wasu batutuwan duniya, kuma tana maida hankali sosai kan muhimmiyar rawar da kasar Sin ke takawa a harkokin duniya. Theresa May ta ce, shawarar 'ziri daya da hanya daya' da shugaba Xi Jinping ya fitar na da babban tasiri a duk duniya, kana, tana fatan kasashen biyu za su inganta hadin-gwiwa a wannan fanni, a wani kokari na raya tattalin arzikin duniya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China