in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD da Red Cross sun yi kira da a tinkari rikicin jin kai
2015-11-01 13:58:36 cri

Babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon da shugaban kwamitin kungiyar Red Cross Terry Morel sun bayar da wata hadaddiyar sanarwa jiya Asabar 31 ga watan Oktoba a birnin Geneva, inda suka yi kira ga kasashen duniya da su maimaita tanade-tanaden da ke cikin kundin tsarin MDD da manyan ka'idojin da ake bi wajen gudanar da ayyukan ba da agaji na Red Cross da Red Crescent, su dauki matakai cikin gaggawa domin tinkarar rikicin jin kai da ake fuskanta a duniya.

Wannan shi ne karo na farko da wadannan manyan hukumomi guda biyu suka ba da hadaddiyar sanarwa cikin hadin gwiwa.

Sanarwa ta yi kira ga kasashen duniya da su rubanya kokarinsu na lalubo bakin zaren hanyar kawo karshen manyan rikice-rikicen da suka barke a duniya, kuma ta kalubalanci bangarorin da rikice-rikicen suka shafa da su bi dokar kasa da kasa da dokar jin kai na duniya. Ban da haka kuma, sanarwar ta zargi hare-haren da aka kai wa fararen hula, ta yi kira da a daina yin amfani da manyan makamai a yankunan dake da yawan mutane, da kara ba da kariya ga masu aikin jin kai, tare da kara dora muhimmanci kan batun 'yan gudun hijira domin kiyaye hakkokinsu da tsugunar da su cikin dogon lokaci yadda ya kamata.

Hakazalika, Ban Ki-Moon ya bayyana wa manema labaru bayan ya sa hannu kan sanarwar cewa, ko ina, ko a yayin ko wane irin rikici, ba za a sa aya ga rikici ta hanyar daukar makamai ba, hanyar siyasa ita ce daidaitacciyar hanyar da za a bi wajen kawo karshensu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China