in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Red Cross ta taka muhimmiyar rawa wajen dakile yaduwar cutar Ebola
2017-06-23 09:49:46 cri

Kungiyar agaji ta Red Cross ta kare sama da mutane 10,000 daga kamuwa da cutar Ebola tsakanin shekarar 2013 da ta 2016 a yankin yammacin Afrika.

Wani rahoto da aka wallafa jiya Alhamis ya ruwaito cewa, tawagar kungiyar a Liberia da Saliyo da Guinea sun yi aiki mai matukar wahala na binne wadanda suka kamu da cutar Ebola, muhimmin mataki amma kuma mai hadarin gaske, la'akari da tasirin kwayar cutar a jikin gawarwaki.

Aikin nasu ya kuma gamuwa da matsala ne daga jana'izar al'ada inda a kan taba tare da wanke gawa, al'amarin da ya taimaka a matakin farko-farko wajen yada cutar.

An wallafa wannan rahoto ne cikin mujallar PLOS, kan cututtukan yankuna masu zafi da aka yi watsi da su.

Rahoton ya kuma gano cewa, binne gawarwakin yadda ya kamata ya kare mutane 10,450 daga kamuwa da cutar, abun da ya rage yaduwar cutar da sama da kashi 36.5.

Tawagar ta Red Cross da suka kunshi masu aikin sa kai 1,500, sun binne mutane 47,000, adadin da ya kai kashi 50 cikin dari na mutanen da aka binne wadanda suka kamu da cutar a lokacin da ta barke. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China