in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta taimaka wajen bunkasa bangaren lafiya a Uganda
2017-09-14 10:34:53 cri

Ministar lafiya ta Uganda Ruth Aceng, ta ce kasar Sin ta zama jigo wajen bunkasa ci gaban bangaren lafiyan kasar.

Ruth Aceng ta bayyana haka ne a jiya, lokacin da take jawabi yayin bikin maraba ga sabuwar tawagar jami'an kiwon lafiya ta kasar Sin a asibitin abota na kasar Sin da Uganda dake birbin Kampala.

Ministar ta ce, suna godiya ga kasar Sin bisa goyon baya da hadin kai da take ci gaba da ba kasar, tana mai yabawa ayyukan da jami'an ke yi a asibitin.

Tawagar jami'an da ta kunshi kwararru 9, za ta yi aiki ne a asibiti mai gadaje 100 da kasar Sin ta ba da gudunmuwarta a shekarar 2012.

Sannan za su gudanar da ayyukan duba lafiya kyauta a kasar dake gabashin Afrika cikin shekaru 2 masu zuwa.

A nasa bangaren, jakadan kasar Sin a Uganda Zheng Zhuqiang ya ce, tura jami'an ya zama daya daga cikin manyan tsare-tsaren kawance ta fuskar kiwon lafiya dake tsakanin Sin da kasashen Afrika.

Kasar Sin ta yi ta tura ayarin jami'an lafiya zuwa Uganda cikin gomman shekaru da suka gabata, da nufin inganta kiwon lafiya a kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China