in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi tir da harin kunar bakin wake da aka kai a Afghanistan
2018-01-29 20:40:10 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying a yau Talata, ta yi tir da harin mota da aka kai a kwanan baya a birnin Kabul, babban birnin kasar Afghanistan, tana mai bayyana cewa, har zuwa yanzu ba a samu rahoton rasuwa ko jikkatar wasu Sinawa ba sakamakon harin.

Hua ta bayyana hakan ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, inda ta kara da cewa, kasar Sin na adawa da duk wani irin aiki na ta'addanci, kuma za ta tsaya tsayin daka kan goyon bayan kokarin da gwamnati da jama'ar Afghanistan suke yi na yaki da ta'addanci, da kiyaye zaman karkon kasar da tsaron jama'a. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China