in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane da dama sun bar gidajensu sakamakon tashe-tashen hankula a gabashin Afghanistan
2018-01-08 10:50:28 cri
Bisa labarin da aka samu a jiya Lahadi, an ce, cikin shekarar 2017 da ta gabata, iyalai sama da dubu 15 sun bar gidajensu a lardin Nanagarhar dake gabashin kasar Afghanistan, sakamakon tashe-tashen hankula a lardin.

A halin yanzu, iyalan suna bukatar taimakon jin kai matuka domin zuwan lokacin sanyi, a sa'i daya kuma, suna sa ran gwamnatin kasar za ta dauki matakai cikin sauri wajen sassauta yanayin tashe-tashen hankula a lardin Nanagarhar, ta yadda za su iya komawa gidajensu cikin sauri.

Bisa labarin da aka samu, an ce, muhimmin dalilin da ya haddasa matsalar shi ne, aukuwar musayar wuta tsakanin kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS, da kuma dakarun Taliban cikin shekarar da ta gabata.

Lardin Nanagarhar shi ne wurin da aka fi fama da matsalolin rikice-rikicen da dakaru ke fafatawa da juna a fadin kasar Afghanistan. Ko da yake, sau da dama, sojojin gwamnatin kasar na mai da martani kan dakarun kungiyar ta IS, amma kungiyar tana ci gaba da kai hare-hare a wurin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China