in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hari ga kudancin kasar Afghanistan
2017-12-18 13:39:49 cri
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Afghanistan suka bayar a ranar 17 ga wata, an ce, dakarun Taliban sun kaddamar da hari a jihar Helmand dake kudancin kasar, wanda ya haddasa mutuwar dakarun kiyaye tsaro 14 tare da raunata wasu guda 3.

Jihar Helmand muhimmin wuri ne dake karkashin ikon kungiyar Taliban, kuma rahotanni sun tabbatar da cewa, a kan aikata laifuffuka masu nasaba da safarar miyagun kwayoyi a wurin. Yanzu haka dai dakarun na Taliban na mallakar a kalla yankuna 6 dake wannan jiha. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China