in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan kalaman tsohon shugaban kasar Obasanjo
2018-01-25 10:31:18 cri

A ranar Laraba ne gwamnatin Najeriya ta mayar da martani ga kalaman da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ya yi, inda ya soki lamarin gwamnatin shugaban kasar Muhammadu Buhari, tana mai cewa, za ta yi la'akari kan shawarar tsohon shugaban kasar.

Lai Mohammed, ministan yada labaran kasar, ya mayar da martani ne bayan kammala taron majalisar zartaswar kasar, inda kuma ya godewa Obasanjo bisa wasikar da ya rubuta.

Shi dai Obasanjo ya yi wasu kalamai ne a cikin budaddiyar wasikar da ya rubuta, wadda ya fitar a ranar Talata, inda ya shawarci shugaba Buhari cewa, kada ya sake tsayawa takarar neman wa'adi na biyu na shugabancin kasar. Ya zargi shugaban kasar da nuna rashin adalci yayin nada jami'ai, da rashin fahimtar siyasa.

Lai Mohammed ya ce, a cikin kalaman na Obasanjo, ya yabawa gwamnatin kasar bisa namijin kokarin da ta yi ta fuskar yaki da 'yan tada kayar baya da yaki da rashawa, wadanda biyu ne daga cikin muhimman bangarori uku da wannan gwamnati ta mayar da hankali kansu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China