in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
LCCI: Masu zuba jari na dari dari sakamakon kalubalen tsaro
2018-01-25 09:15:19 cri

Cibiyar hada hadar cinikayya da masana'antu ta jihar Lagos dake tarayyar Najeriya, ta nuna damuwa game da yadda kalubalen tsaro a wasu yankunan kasar ke sanya masu sha'awar zuba jari ja da baya.

Shugaban cibiyar ta LCCI Babatunde Ruwase ne ya bayyana hakan a jiya Laraba, yayin wani taron karawa juna sani game da yanayin da Najeriyar ke ciki. Mr. Ruwase ya ce, akwai bukatar gwamnati ta sake nazartar batun tsaro, ta kuma kara dora muhimmanci kan matakan kare rayuka da dukiyoyin al'ummar kasar.

Ya ce, aukuwar muggan laifuka kamar ayyukan kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, da kashe kashe masu nasaba da rikicin makiyaya da manoma, da garkuwa da mutane, da fashi da makami, da ayyukan matsafa na matukar barazana ga tsaron kasa.

Kaza lika a cewar sa fadace fadacen addini da na kabilanci na dada yaduwa a kasar, kuma muddin ba a magance hakan ba, fatan da ake yi na samar da isasshen abinci ga 'yan kasar ba zai cika ba.

Mr. Ruwase na ganin karancin abinci kuwa zai haifar da hauhawar farashin sa a kasuwanni, da karancin amfanin gona da za a rika bukata domin sarrrafawa a masana'antu. Har ila yau hakan na iya sanya masu zuba jari dari dari ga batun sanya jari a Najeriya, baya ga tasirin da hakan zai yi ga kimar kasar a idanun duniya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China