in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta hukunta masu safarar bil adama zuwa Libya
2018-01-10 10:44:29 cri

Wata babbar jami'a a hukumar yaki da safarar bil adama ta Najeriyar ta bayyana cewa, kasar za ta hukunta dukkan wadanda aka samu da hannu wajen yin safarar 'yan Najeriyar zuwa kasar Libya.

Julie Okah-Donli, darakta janar ta hukumar haramta safarar bil adama ta Najeriya (NAPTIP), ta shedawa manema labarai cewa, bayanai game da yadda mutanen ke zuwa kasar Libya da wadanda suke daukar nauyinsu za'a bi diddigi don gano masu ruwa da tsaki a yin safarar da kuma hukunta su yadda ya kamata.

Daraktar ta ce, a halin yanzu jami'anta suna kasar ta Libya inda suke tattaro dukkan muhimman bayanai game da masu daukar nauyin safarar 'yan Najeriyar.

Ta ce, idan har aka gano wani da yake yin safarar a Libya, kuma ya nuna ba shi da sha'awar dawowa gida, to za'a tusa keyarsa kuma a yanke masa hukunci a Najeriyar.

Okah-Donli, wanda tana daga cikin tawagar jami'an gwamnati wadanda suka jagoranci kwashe 'yan Najeriyar 972 daga kasar Libya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a kafa wata cibiya a kudancin birnin Fatakol don kula da wadanda aka kwaso.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China