in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya yi watsi da zargin tsame makiyaya daga kaddamar da hare hare
2018-01-10 10:38:19 cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, tsagwaron rashin adalci ne da rashin kirki a yada jita-jitar cewa shugaban yana wanke makiyaya daga zargin hare haren wadanda suka yi sanadiyyar hallaka rayuka masu yawa a kasar.

Cikin wata sanarwa, shugaban na Najeriya ya ce, a shirye yake ya dauki dukkan matakan da za su kawo karshen kashe kashen rayuka a kasar.

Shugaba Buhari ya ce, gwamnatinsa a shirye take ta bi dukkan matakai na kusa da na nesa wadanda za su warware matsalolin fadace-fadace tsakanin makiyaya da manoma a duk fadin kasar.

Tun shigowar sabuwar shekarar nan ake ta samun karuwar kashe kashen rayukan wadanda ake danganta su da makiyaya a jihar Benue, kana ana ci gaba da samun tsamin dangantaka tsakanin makiyaya da manoma, yayin da a wasu jihohin da suka hada da Kaduna, Kwara da jihar Rivers, an samu kashe-kashe masu yawa.

An ayyana ranar Alhamis ta zama ranar hutu a jihar Benue domin ma'aikata su samu damar halartar jana'izar mutanen da aka hallaka, kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar.

A ranar Talata shugaba Buhari ya ba da umarni ga babban sifeton 'yan sandan kasar da ya koma jihar ta Benue dake shiyyar arewa da tsakiyar Najeriyar don kawo karshen tashin hankalin.

Jihar ta Benue ta kafa dokar haramta kiwo a filiye a ranar 1 ga watan Nuwambar shekarar 2017, lamarin da ya haifar da bore daga makiyaya a jihar.

Daruruwan mutane ne aka kashe a hare haren da ake danganta su da makiyaya a jihohin Benue, Nasarawa da Plateau a shekarar da ta gabata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China