in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF: matsalar rashin tabbas game da harkokin kudade zai iya haifar da gibi wajen farfadowar tattalin arzikin duniya
2017-10-12 10:24:08 cri
A jiya Laraba, asusun ba da lamuni na duniya, IMF ya ce, yanzu ana ta samun kyautatuwar halin hada hadar kudi a duk fadin duniya, amma IMF ya yi gargadin cewa matsalar rashin tabbas game da harkokin kudade zai iya haifar da gibi wajen farfadowar tattalin arzikin duniya

A cikin "rahoto game da halin rashin tabbas na harkokin kudade na duk duniya" da IMF ya wallafa a jiya, an ce, yanzu muhimman kungiyoyin tattalin arziki na ci gaba da aiwatar da manufar kudi mai sassauci, wannan yana taimakawa wajen karuwar tattalin arziki, da kuma mayar da mizanin raguwar darajar kudi a wani wurin da ake bukata, amma a waje daya, zai sanya a martaba kadarorin duk duniya fiye da kima.

Sannan rahoton ya nuna cewa, yawan basusukan da manyan kungiyoyin tattalin arziki suka sha na ci gaba da karuwa, wannan kuma zai kawo illa ga bunkasuwar tattalin arzikin duk duniya baki daya.

Bugu da kari, IMF ya ce, idan mizanin raguwar darajar kudi ya karu cikin sauri fiye da kima, muhimman manyan bankunan kasashen duniya ma sun tsuke bakin aljihu game da harkokin kudi ba zato ba tsammani, maiyiwuwa ne za a ta da tarzoma a kasuwar hada hadar kudi. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China