in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya yi hasashen samun ci gaban tattalin arzikin kaso 2.7 a kudu da hamadar Sahara
2017-10-31 10:17:10 cri
Wani rahoton da bankin bada lamuni na IMF ya fitar, ya yi hasashen samun ci gaban tattalin arziki na kaso 2.6 bisa dari, a kudu da hamadar saharar Afirka, adadin da ya dara kaso 1.4 bisa dari da yankin ya samu a bara.

IMF ya ce hakan ya biyo bayan karuwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya, wanda kasashe kamar Najeriya za su ci gajiyar sa, da kuma raguwar fari a yankunan gabashi da kudancin Afirka.

Har wa yau IMF din ya ce akwai yiwuwar ci gaban tattalin arzikin yankin na kudancin Saharar Afirka ya karu zuwa kaso 3.4 a shekarar 2018 dake tafe, duk da cewa yanayin tafiyar hawainiya zai wanzu ya zuwa shekarar 2019.

A cewar daraktan nahiyar Afirka na IMF Abebe Aemro Selassie, daya bisa uku na kasashen wannan yanki dake gabashi da yammacin Afirka, za su ci gaba da samun ci gaban da zai kai kaso 5 ko fiye da hakan a lokutan da aka zayyana, yayin da adadin kudaden shigar al'umma zai ragu a kasashen yankin 12, kimanin kaso 40 bisa dari na daukacin kasashen shiyyar, ko kusan mutum miliyan 400 ke cikin wannan rukuni. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China