in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun bada lamuni na duniya ya ce musayar takardar kudin RMB na kasar Sin na bisa ka'ida
2017-07-29 13:20:32 cri

Asusun bada lamuni na duniya IMF ya ce musayar takardar kudin RMB ta kasar Sin ya yi daidai da ka'idoji da manufofi da aka gindaya.

A cewar rahoton da asusun ya fitar a jiya Jumma'a, a bara, musayar ta sauka da kimanin kashi 5.1 idan aka kwatanta da shekarar 2015 inda take kara karfi tare da dalar Amurka.

Shugaban sashen bincike na asusun Luis Cabeddu, ya ce dabarun da kasar Sin ta dauka domin daidaita habakar kudin ne ya janyo tagomashin da RMB ya samu, tare da taimakawa wajen saukaka fitar kudade da raguwar asusun ajiya na waje.

Asusun ya kuma kara da cewa, rashin daidaito da kasar ke fuskanta ya ragu tun bayan matsalar kudi da aka shiga a duniya.

Asusun ya yi hasashen cewa, asusun rara na kasar Sin zai ci gaba da raguwa idan ta ci gaba da aiwatar da manufofinta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China