Ministan harkokin wajen kasar Algeria Ramtane Lamamra ya ce, majalisar dinkin duniya na aiwatar da shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya guda tara a nahiyar Afrika.
Da yake ganawa da manema labarai a wani bangare na wani taron bita kan tsaro a Algeria, ministan ya ce, daga cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya goma sha shida da majalisar ke aiwatarwa a fadin duniya, guda tara sun kasance a nahiyar Afrika
Ya ce, dole ne majalisar ta kara karfafa hadin kai da hukumomin tarayyar Afrika a wannan tsari, domin samun ingantaccen zaman lafiya mai dorewa.
Baya ga shirin MINURSO mai shirya yarjejeniyar zaman lafiya a yankin yammacin Sahara dake fama da rikice-rikice, sauran wurare takwas da ake aiwatar da shirye-shiryen sun hada da Liberia, da Cote d'Ivoire, da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da Sudan, da Sudan ta Kudu, da Darfur, da Mali, da kuma Afrika ta Tsakiya. (Fa'iza)