in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar wakilan Algeria ta amince da kasafin kudin kasar na badi
2017-11-27 10:36:33 cri

Majalisar wakilan kasar Algeria, ta amince da kudurin kasafin kudin kasar na shekarar 2018 a jiya Lahadi.

Kamfanin dillancin labaran kasar na APS ya ruwaito cewa, kasafin ya kunshi jerin manufofin doka da na harkokin kudi wadanda ke da nufin karfafa hanyoyin zuba jari da harkokin da suka shafi kudaden shiga da kudaden da za a kashe, yayin da zai kuma tabbatar da dorewar matakan ciyar da kasar gaba.

Kasafin ya kai kimanin dala biliyan 133, yayin da gibin ya ragu daga kaso 14 na alkaluman GDP a shekarar 2016 zuwa kaso 9 a 2018.

Kudin da za a kashe kan manyan ayyuka da ayyukan yau da kullum, ya kai kimanin dala biliyan 76, yayin da aka yi kiyasin kudaden shiga za su kai kimanin dala biliyan 57.

Sai dai majalisar ba ta amince da sanya haraji kan dukiya ba, kamar yadda gwamnati ta gabatar cikin kudurin.

Duk da matsalar kudin da kasar ke ciki saboda raguwar kudaden shiga tun daga shekarar 2014, wanda a karshen bana zai kai kusan dala biliyan 31, kasafin kudin na badi ya ware kimanin dala biliyan 16 ga ayyukan tallafawa al'umma.

Tallafin zai tafi ne kai tsaye ga tsarin tallafawa iyalai marasa karfi da shirye-shiryen samar da gidaje da kiwon lafiya, baya ga rage farashin kayayyakin da aka fi amfani da su kamar alkama da suga da man girki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China